2 Yuni 2021 - 13:19
Imam Khamenei Zai Yi Jawabi A Ranar Juyayin Cika Shekaru 32 Da Wafatin Imam Khomaini

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zai yi jawabi ga mutane ta tasoshon talabijin na kasar a ranar jumma’a 4 ga watan Yuni wato shekaru 32 da rasuwar Imam Khomaini (q) wanda ya jagoranci kafa JMI a shekara 1979. Imam ya rasu a ranar 4 ga watan Yunin Shekara ta 1989.

ABNA24 : Ana saran za’a watsa jawabin nasa kai tsaye daga tashoshin talabijin da radiyo da dama, daga ciki har da hausa tv VOH da harshen hausa, da kuma Pressrv da harshen turanci, sannan Al-alam da harshen larabci. Zai yi jawabin ne kai tsaye da misalign karfi 11 na safe a nan Tehran, sannan karfe 2.30 na rana agogin Najeriya da Niger. 1.30 agogon Ghana.

342/